Tuesday 2 December 2025 - 20:15
Ayyuka da Albarkar Jami'ar Az-Zahra (AS) Suna Da Yawa Kuma Suna da Tasiri

Hauza/ Shugaban makarantun ilmin addinin Musulunci (Hauza) na ƙasar Iran ya yi nuni da fa'ida da albarkar da Jami'ar Az-Zahra (AS) ke samarwa, kuma ya jaddada muhimmancin rawar da cibiyar ke takawa wajen horar da ma'aikata masu inganci, da kuma buƙatar ƙarin tallafi da kayan aiki don haɓaka ayyukanta.

A rahoton wakilin ofishin dillancin labaran Hauza, Ayatullah Alireza A'arafi, shugaban makarantun ilmin addini (Hauza) na ƙasar Iran, a yayin ganawa da membobin hukumar gudanarwar Jami'ar Az-Zahra (AS), ya nanata muhimmin matsayi da kuma rawar da cibiyar ke takawa a fagen ilimantar da mata malamai.

Shugaban Kwamitin Tsare-Tsare na Makarantun Ilmn Addini ta Mata, ya yi godiya ga membobin Hukumar Gudanarwar Jami'ar Az-Zahra (AS), ya ce: "Ina yaba wa babban kokarin da Hukumar Gudanarwa mai girma da manajoji na wannan cibiyar suke yi, domin gudanar da cibiya mai girma kamar wannan, mai ayyuka iri-iri, shirye-shirye daban-daban, ta bangaren yawa da inganci, aiki ne mai nauyi kuma mai daraja."

Shugaban Makarantun Addini na Ƙasar, ya bayyana cewa kallonsa ga makarantun addini na mata kallo ne mai zurfi, ya kara da cewa: "Girman aikin da Jami'ar Az-Zahra (AS) ta ke yi da kuma rawar da za ta iya takawa a nan gaba, yana da ban mamaki kuma ba zai kwatantu ba; har a wasu fagage, sakamakon da albarkar wannan cibiya ke samarwa yana da yawa kuma yana da tasiri."

Ya ci gaba da nuni da tallafin da ya kasance yana ba wa Jami'ar ta Az-Zahra (AS), ya ce: "A cikin shekarun da suka gabata, sau da yawa a cikin tarurruka daban-daban da kuma a cikin wasu mas'ulan da ba su da cikakkiyar masaniya game da Jami'ar Az-Zahra (AS), na sha kare wannan cibiyar ta ilimi, kuma yanzu ma a cikin tarurruka daban-daban ina jaddada wajabcin tallafa wa wannan cibiya. Na yi imani cewa Jami'ar Az-Zahra (AS) kamar sauran cibiyoyin koyarwa na makarantun addini, yakamata a ba ta cikakken tallafi."

Ayatullah A'arafi ya bayyana makomar Jami'ar Az-Zahra (AS) a matsayin mai haske kuma mai ci gaba, ya ce: "Ina kallon Jami'ar Az-Zahra (AS) a matsayin wata kololuwa a cikin cibiyoyin makarantun addini na mata; wata kololuwa da zata iya buɗe sabbin fagage kuma ta horar da manyan mutane masu tasiri. Wannan hanya, godiya ga Allah, tana ci gaba, kuma idan aka ƙara kayan aiki da tallafi, ƙarfin wannan cibiya zai fi yadda yake a yanzu."

A farkon ganawar, Dokta Birƙa'i, Shugabar Jami'ar Az-Zahra (AS), ta gabatar da rahoto game da tsarin ayyukan Hukumar Gudanarwa da halin da wannan cibiyar addini ke ciki.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha